in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ana ci gaba da shawarwari kan batun Syria a Geneva
2017-12-06 11:13:33 cri
Jiya Talata, aka sake dawo teburin shawarwari kan batun Syria a birnin Geneva, bayan a karshen makon da ya gabata aka dakatar da zaman na dan wani lokaci. Haka kuma, manzon musamman na babban magatakardan MDD dake kula da batun Syria Staffan de Mistura ya gana da wakilan kungiyar adawa.

Kamar yadda MDD ta tsara, an shirya yin shawarwari tsakanin wakilan gwamnatin kasar Syria da na kungiyar adawa a karshen makon da ya gabata. Haka kuma wakilan gwamnatin kasar sun koma birnin Damascus domin kara tattaunawa da jami'an gwamnati kan wannan batu.

Kaza lika, bisa sabon shirin MDD, za a tsawaita taron shawarwarin neman sulhu kan batun Syria zuwa ranar 15 ga watan nan da muke ciki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China