in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Syria ta yi maraba da tattaunawar Sochi game da yadda za a warware rikicin kasar
2017-11-23 10:46:18 cri

Jiya Laraba, ma'aikatar harkokin wajen kasar Syria ta ce ta yi maraba da sakamakon tattaunawar da shugabannin kasashen Rasha da Iran da Turkiya suka gudanar a birnin Sochi na kasar Rasha kan yadda za a warware rikicin kasar.

Sanarwar ta ce, an sanar da sakamakon karshe na tattaunawar da shugabannin kasashen uku suka yi ne, bayan wata ganawa da shugaba Bashar al-Assad na Syria ya yi da takwaransa na kasar Rasha Vladimir Putin kwanaki biyu da suka gabata a birnin na Sochi. Wannan ya nuna cewa, yadda Syria ta goyi bayan ganawar, wata alama ce ta zakuwar gwamnatin Syria na ganin an kawo karshen rikicin kasar ta hanyar matakan siyasa.

A sanarwar bayan taron da aka fitar, shugabannin uku sun goyi bayan yin tattaunawa a Syria, sun kuma yanke shawarar ci gaba da hada kai don ganin bayan kungiyar IS a Syria.

A jiya ne dai shugabannin Rasha da Turkiya da Iran suka gana a birnin na Sochi don tattauna matakan magance rikicin kasar ta Syria.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China