in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Manzon musamman na MDD ya bukaci bangarorin Syria da su daina gindaya sharadi
2017-11-30 11:12:40 cri
Shawarwari zagaye na 8 da ake gudanarwa tsakanin bangarorin kasar Syria, karkashin jagorancin MDD, sun shiga kwana ta 2 a jiya Laraba.

A wajen taron, manzon musamman na babban magatakardan MDD mai kula da batun Syria Staffan de Mistura, ya bukaci gwamnatin kasar Syria da kungiyoyin masu adawa, da su gudanar da shawarwari ba tare da gindaya sharadi ba, ta yadda za a samu takamaiman ci gaba a shawarwarin.

A yammacin ranar Laraba, mista Mistura ya gana da tawagar gwamnatin kasar Syria, inda ya ce wannan ganawa tana tare da ma'ana da sakamako, sai dai ya ki bayyana ainihin sakamakon da aka samu.

Shi dai mista Mistura bai bayyana tsawon kwanaki da tawagar za ta yi tana zama a Geneva, da ma batun ko za ta yi shawarwari kai tsaye tare da masu adawa da gwamnati ba tukuna.

Cikin wata sanarwar da mista Mistura ya gabatar duk dai a ranar ta Laraba, ya bukaci bangarorin Syria da su dakatar da dora wa juna laifi, inda ya ce gudanar da shawarwari yadda ya kamata, shi ne zai tabbatar da moriyar jama'ar kasar Syria.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China