in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta kai taimakon tan dubu na shinkafa kasar Syria
2017-11-21 11:58:01 cri
A jiya ne kasar Sin ta baiwa yankin Latakia dake arewa maso yammacin kasar Syria gudummawar tan dubu daya na shinkafa, kamar yadda ofishin jakadancin kasar ta Sin dake Damascus ya bayyana a cikin wata sanarwa.

Sanarwar ta ce, wannan gudummawa, wani bangare ne na tan dubu 5,404 na shinkafa da kasar Sin ta yi alkawarin bayarwa nan gaba.

Mahukuntan Kasar Sin na aiki kafada da kafada da bangaren kasar Syria don tabbatar da cewa, shimkafar da aka bayar ya shiga hannun al'ummar Syria ba tare da wani bata lokaci ba.

Da ya ke karbar gudummawar, gwamnan yankin Latakia Ibrahim Khudr Salem, ya bayyana godiya da tallafin kayan abincin da kasar Sin ta samar musu.

A jiyan ne dai wata tawaga daga ofishin jakadancin kasar Sin dake Damascus ta ziyarci tashar jiragen ruwa dake birnin Latakia a yankin arewa maso yammacin kasar ta Syria domin mika kashin farko na shinkafar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China