Rahotanni sun ce, gwanmatin kasar ta tsai da kudurin ne bayan ta tattauna da bangaren Rasha, inda kuma aka ba zaunannen wakilin kasar Syria a MDD Bashar al-Jaafari jagorancin tawagar wakilan.
A nasa bangare kuma, manzon musamman na babban magatakardan MDD dake kula da batun Syria Staffan de Mistura, ya ce, ya riga ya samu labarin cewa, wakilan gwamnatin Syria za su halarci taron a yau Laraba 29 ga wata.
Bayan ganawarsa da tawagar wakilan jam'iyyun adawa da gwamnatin Syria, Mr. Mistura ya ce, mai yiyuwa ne, wakilan gwamnatin Syria da wakilan jam'iyyun adawa su hau teburin sulhu kai tsaye a karo na farko yayin taron. (Maryam)