in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jami'in MDD: Za'a ci gaba da tattaunawa kan batun Syria zuwa 15 ga watan Disamba
2017-12-01 10:34:06 cri

Wakilin musamman na MDD a kasar Syria Staffan de Mistura, ya bayyana cewa, yana shirye shiryen tsawaita wa'adin tattaunawar da MDDr ke jagoranta kan wanzar da zaman lafiya a Syria zuwa ranar 15 ga watan Disamba.

Sabon zagayen tattaunawar an fara shi ne a ranar Talata, da farko an tsara tattauanwar ne a ranar 1 ga watan Disamba.

Da yake jawabi ga manema labarai game da batun tattaunawar rikicin na Syria wanda aka fara a Geneva, wanda ake tsammanin samun sakamako marar tasiri, De Mistura, ya bayyana tattaunawar ta wannan mako da cewa muhimmiya ce kuma mai inganci.

De Mistura ya bayyana yanayin tattaunawar da cewa ya sha bamban da lokutan baya ta ko wace fuska.

A cewarsa, babban kalubale shi ne na rashin amincewa, wanda ya bayyana shi a matsayin abin da ya saba faruwa a tattaunawar sulhun kan rikicin na Syria. Ya ce dole ne a lalubo matakan tattaunawar ta hanyar siyasa, bai dace a yi amfani da matakin soji ba.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China