A jiya ne, aka fitar da rahoton bunkasuwar intanet na kasashen duniya na shekarar 2017 da kuma rahoton bunkasuwar intanet na kasar Sin na shekarar 2017, wadanda suka nuna yanayin bunkasuwar harkokin intanet a kasashen duniya da kuma ci gaban da kasar Sin ta samu sakamakon amfani da intanet.
Haka kuma, cikin tahotannin da aka fitar, an tsara wani shirin yin bincike kan yanayin bunkasuwar intanet, inda aka shigar da kasashe guda 38 cikin jerin kasashen da suka samu ci gaba a fannin intanet. (Maryam)