Karkashin sabuwar dokar wadda majalisar zartaswar kasar ta amince da ita a watan Nuwamban shekarar da ta gabata, an haramtawa masu bayar da layin intanet tattara bayanan jama'a da ba su da nasaba da hidimomin. Haka kuma su rika kula da wadannan bayanai kamar yadda doka da kuma yarjejeniyar da aka kulla tsakanin bangarorin biyu suka tanada.
A saboda haka, yanzu masu amfani da intanet suna da ikon tambayar masu samar musu hidima da su goge musu bayanansu idan har sun ci zarafin bayanan nasu.
Bugu da kari, wajibi ne ma'aikatan dake kula da tsaron intanet su kare bayanan da ke shigo musu, kana an haramta musu bayyana ko sayar da muhimman bayanai, ciki har da kare kima da martaba da sirrin harkokin kasuwanci.
Dokar ta ce, duk wanda aka kama yana karya tanade-tanaden dokar, sannan ya bayyana muhimman bayanai da aka haramta, to za a ci tararsa. Haka kuma dokar ta bayyana karara cewa, ba a yarda kowanne mutum ya yi amfani da intanet wajen aikata zamba ko sayar da kayayyakin da doka ta haramta ba.
Akwai wasu dokoki da ake sa ran za a bayyana a ranar 1 watan Yuni game da wannan doka. (Ibrahim Yaya)