Wata sanarwar hadin gwiwa da Gwamnatocin kasashen biyu suka fitar a jiya Juma'a, ta zayyana muhimman sakamakon da aka samu yayin tattaunawa kan aiwatar da dokoki da tabbatar da tsaron kafar intanet tsakanin kasar Sin da Amurka da aka yi karon farko a ranar Laraba da ta gabata.
Sanarwar ta ruwaito bangarorin biyu na bayyana niyyarsu ta inganta hadin gwiwa kan tabbatar da takaita safara da sarrafa miyagun kwayoyi.
Sin da Amurka sun kuma amince su ci gaba da aiwatar da batutuwan da suka cimma a shekarar 2015 kan hadin gwiwa ta fuskar tsaron kafar intanet, ciki har da yarjejeniyar da suka kulla cewa, babu Gwamnatin wata kasa cikinsu da za ta goyi bayan kutsen intanet don satar wani muhimmin abu alhali ta na sane. (Fa'iza Mustapha)