Mistan harkokin sadarwa na kasar Adebayo Shittu, ya fadawa manema labarai a jiya Juma'a cewa, dole ne a hada hannu don magance duk wani nau'in kutsen intanet a kasar, yana mai cewa, daidaikun mutane har ma da ma'aikatu na iya fadawa tarkon masu kutsen.
Ya ce idan aka shiryawa tunkararsu, to illa da za su yi ba za ta yi yawa ba.
Ministan ya ce tunanin cewa gwamnati ce ke da hakkin shiryawa tunkarar matsalar ba daidai ba ne, ya na mai cewa hadin gwiwa shi ne hanya mafi dacewa ta yaki da ko wani irin nau'i na kutsen intanet a kasar, tun da har kasashen da suka ci gaba ma ba su tsira ba. (Fa'iza Mustapha)