Rahotanni na cewa, kasar Sin ce za ta karbi bakuncin taron Intanet na duniya karo na 4 (WIC) da zai gudana a wata mai zuwa a birnin Wuzhen dake lardin Zhejiang a kudu maso gabashin kasar Sin.
Wata sanarwa da aka wallafa a shafin na WIC ta nuna cewa, taron wanda zai gudana daga ranar 3 zuwa 5 ga watan na Disamba, ya gayyaci masu ruwa da tsaki daga gwamnatoci da kungyoyi masu zaman kansu da na kasa da kasa da kamfanoni da masana harkar Intanet, inda za su tattauna batutuwan da suka shafi harkokin tattalin arziki ta yanar gizo, ci gaban fasahohin zamani, tsaron Intanet da sauransu.
Bugu da kari, taron na wannan shekara zai gabatar da sabbin fasahohin da aka samu a fannin Intanet a duniya, da bukatar gina duniya mai kyakkyawar makoma a fannin fasahar yanar gizo, mutunta juna, da mayar da hankali kan harkokin ci gaba da kirkire-kirkire, ta yadda fasahar Intanet za ta inganta rayuwar dan-Adam.
Hukumar kula da harkokin Intanet ta majalisar gudanarwar kasar Sin da gwamnatin lardin Zhejiang ne suka dauki nauyin taron na bana.(Ibrahim)