Jami'an yan sandan kasar Sin sun yi nasarar warware matsaloli da suka shafi aikata ha'inci ta hanyoyin sadarwa da internet 83,000 a shekarar 2016, adadin wanda ya kai kashi 49.6 bisa 100 da ake samu a duk shekara.
Ma'aikatar ta bayyana cewar ana samun raguwar adadin aikata laifukan a duk shekara tun daga watan Satumbar bara.
MPS ta ce an samu nasarar kashe kaifin yawaitar aikata laifukan yin zamba ta hanyar sadarwar da internet. Hasarar da ake samu ta bangaren zamba ta hayar sadarwar da internet ya ragu da kashi 10.9 a 2016 idan aka kwatanta da na shekarar 2015.
A cewar ma'aikatar, yan sanda sun yi nasarar dakatar da aika kudade ta hanyar bankuna kimanin miliyan 1.55 wadanda suke da nasaba da yin al-mundahana, adadin kudin da ka kiyasta ya kai yuan biliyan 5 kwtankwacin dalar Amurka miliyan 730 tun daga lokacin da aka yi hadin gwiwa tsakanin yan sanda da bankunan. (Ahmad)