Rahoton mai taken yadda al'ummar duniya ke cin gajiyar tsarin intanet na shekarar 2017: tasirin intanet a kokarin samun ci gaba mai dorewa, an yi kiyasin cewa, ya zuwa karshen shekarar 2017 da muke ciki, za a samu mutane biliyan 3.58 da za su rika amfani da tsarin Intanet, daidai da kaso 48 cikin 100 na yawan al'ummar duniya, wato kari kan mutane biliyan 3.4 ko kuma kwatankwacin kaso 45.9 cikin 100 a karshe shekarar 2016 da ta gabata.
Yanzu haka dai hankali ya karkata ne kan ragowar mutanen da ba sa cin gajiyar wannan tsari, yayin da kusan rabin al'ummar duniya ke amfani da yanar ta gizo.
Sai dai kungiyar sadarwa ta kasa da kasa(ITU) ta yi kiyasin cewa, ya zuwa karshen wannan shekara ta 2017, yadda ake amfani da intanet a kasashe masu tasowa zai kai kaso 41.3, kwatankwacin yadda aka samu kaso 39 cikin 100 a karshen shekarar 2016 da ta gabata. Sai dai idan aka kwatanta da yadda ake amfani da intanet a kasashe takwarorinsu da suka ci gaba,zai kai kaso 81 cikin 100, yayin da matsakaicin amfani da intanet a duniya baki daya ya kai kaso 48 cikin 100.(Ibrahim)