Haka kuma, ya bayyana wa kafofin watsa labarai cewa, sabuwar majalisar ministocin ta wannan karo za ta kammala wa'adin aikinta bayan babban zaben da za a yi a shekara mai zuwa, lamarin da ya nuna cewa, wa'adin aikinta ya wuce watanni shida. Sa'an nan, ya yi kira ga al'ummomin kasar da su nuna tabbaci ga sabuwar gwamnatin kasar, gwamnatin kasar za ta hada kai da dukkanin al'ummomin kasar wajen raya tattalin arziki da kuma samar da karin guraben ayyukan yi. (Maryam)