in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Zimbabwe za ta sake nazarin dokar mallakar kadarori
2017-12-01 13:04:27 cri
Mukaddashin Ministan kudin Zimbabwe Patrick Chinamasa, ya ce kasar za ta sake nazarin dokar mallakar kadarori mai sarkakiya, domin sauya yanayin harkokin tattalin arziki da kuma jan hankalin masu zuba jari.

Yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a jiya Alhamis, Patrick Chinamasa ya ce Gwamnati za ta gaggauta daidaita dokar mallakar kadarorin da wasu manufofin da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ya sanar a bara.

Da yake fayyace dokar biyo bayan bahaguwar fahimtar da wasu ministocinsa suka yi, Robeert Mugabe, ya ce za a cire wuraren hakar ma'adinan da ake da su wadanda har yanzu ba a mallake su ba daga cikin wadanda ake bukatar mallakar kaso 51,amma za a rike kaso 71 na jimilar kudin shigarsu a matsayin kudin albashi da haraji da kuma na sayen kayayyaki.

Sai dai, a sabon shirin zuba jari na bangaren hakar ma'adinai, Gwamnati da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki za su mallaki kaso 51 yayin da masu zuba jari za su mallaki sauran kaso 49.

Ministan ya ce za a daidaita dokar mallakar kadarori da karfafa harkokin tattalin arziki da wadancan manufofi na Mugabe nan ba da dadewa ba, saboda an zartar da su amma kuma Ministan kula da harkokin mallakar kadarori na wancan lokaci ya gaza aiwatarwa da su. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China