Sanarwar da sakataren shugaban kasar Misheck Sibanda ya fitar, ta ce Shugaba Emmerson Mnangagwa ya nada Patrick Chinamasa a matsayin mai rikon mukamin ministan Kudi yayin da ya nada Simbarashe Mumbengegwi a matsayin ministan harkokin waje, domin bada damar gudanar da ayyuka ba tare da tangarda ba a muhimman ma'aikatun gwamnatin har zuwa lokacin da za a nada sabbin ministoci.
A baya, ministocin biyu sun taba rike ma'aikatun, kafin tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ya sauya musu a watan Oktoban, biyo bayan tangade da rairaya da ya yi ga majalisar zartaswar.
Sanarwar ta kara da cewa, a yau Talata ne Shugaba Mnangagwa zai gana da dukkan manyan sakatarorin gwamnati.
An rantsar da Emmerson Mnangagwa matsayin shugaban kasar ne a ranar Jumma'a da ta gabata, bayan tsohon shugaba Robert Mugabe ya yi murabus biyo bayan matsin lamba da ya fuskanta daga sojoji da al'ummar kasar. (Fa'iza Mustapha)