in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin musamman na kasar Sin ya isar da sakon Xi Jinping ga shugaban Zimbabwe
2017-11-30 18:43:45 cri
Wakilin musamman na gwamnatin kasar Sin, kana mai taimakawa ministan harkokin wajen kasar, Chen Xiaodong, ya ziyarci Zimbabwe bisa gayyatar gwamnatin kasar. Game da wannan batu, mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen Sin, Geng Shuang ya ce, Chen ya ziyarci sabon shugaban Zimbabwe, Emmerson Mnangagwa ne, domin mika sakon shugaba Xi Jinping ga shugaba Mnangagwa, inda ya taya shi murnar zama shugaban kasar. Kasar Sin ta yi imanin cewa, babu tantama ziyarar Chen a wannan karo za ta kara karfafa dankon zumunci tsakanin Sin da Zimbabwe.(Murtala Zhang)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China