in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bayyana tabbacin ci gaban kasar Zimbabwe
2017-11-27 18:21:32 cri
Kasar Sin ta bayyana tabbacinta game da ci gaban kasar Zimbabwe, yayin da sabon shugaban kasar Emmerson Mnangagwa ya yi alkawarin kare jarin da kasashen duniya suka zuba a kasar.

Mai Magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang wanda ya bayyana hakan yau Litinin yayin taron manema labarai a nan birnin Beijing, ya ce kasar Sin tana goyon bayan matakan da Zimbabwe ta dauka wanda ya dace da yanayin da take ciki wajen raya kanta. Ta kuma yi imanin cewa, kasar za ta samu gagarumin ci gaba karkashin jagorancin shugaba Mnangagwa.

Bugu da kari, kasar Sin tana fatan karfafa alakar dake tsakaninta da Zimbabwe bisa tushen daidaito da samun moriya tare.

Ya ce, kasar Sin za ta yi duk abin da ya dace bisa karfinta wajen ganin ta taimakawa kasar Zimbabwe farfado da tattalin arzikinta tare da inganta rayuwar jama'a.

A ranar Jumma'ar da ta gabata ce aka rantsar da Emmerson Mnangagwa a matsayin shugaban kasar ta Zimbabwe, inda ya yi alkawarin cewa, babu abin da zai taba jarin da kasashen ketare suka zuba a kasar, kuma, Zimbabwe za ta taka rawa a harkokin kasa da kasa da na shiyya-shiyya. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China