Ya ce, cikin 'yan shekarun nan, 'yan ta'adda sun yi ta kai hare-haren ta'addanci a wasu kasashen duniya, a sa'I daya kuma, suna samun kyautatuwa a fannonin yin mu'amala da kuma gudanar da aikace-aikacen ta'addancin da abin ya shafa. Don gane da wannan lamari, kasar Sin ta bayar da shawarwari guda uku, domin dakile ayyukan ta'addanci a tsakanin kasa da kasa.
Da farko, a dauki matakai yadda ya kamata wajen hana 'yan ta'adda yin tafiye-tafiye a tsakanin kasa da kasa, na biyu shi ne, a karfafa ayyukan yaki da masu aikata laifin ta yanar gizo, na uku shi ne, a girmama al'adun juna, ta yadda za a kawar da matsalar daga tushe.
Mr. Wu ya kara da cewa, kasar Sin tana adawa da duk wani nau'i na ta'addanci, kuma, a matsayin babbar mamba ta bangaren yaki da ta'addanci na kasa da kasa,kasar Sin za ta dukufa wajen shiga ayyukan yaki da ta'addanci da MDD, kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai da kuma dandalin yaki da ta'addanci na kasa da kasa suka shirya.
Bugu da kari, kasar Sin za ta yi hadin gwiwa da kasashe da kuma kungiyoyin da abin ya shafa wajen fuskantar kalubalolin dake shafar ta'addanci, ta yadda za a tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a kasashen duniya. (Maryam)