Bayan aukuwar harin, shugaban kasar Masar Abdel Fattah al Sisi, ya kira wani taron gaggawa na kwamitin yaki da ta'addanci na kasar, domin tattauna yadda za a fuskanci harin da aka kai kasar.
Da yake jawabi ta gidan talabijin na kasar, Shuagaba Al Sisi ya ce za a dauki matakan mai da martani kan maharan ba tare da bata lokaci ba, sannan rundunar soji da ta 'yan sandan kasar za su dukufa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duk fadin kasar cikin gaggawa.
Shugaban ya kuma yi wa iyalan wadanda suka rasa rayukansu ta'aziyya tare da yi wa wadanda suka jikkata fatan samun sauki cikin sauri.
Tun da farko, Gwamnatin kasar Masar ta sanar da ayyana zaman makoki na kwanaki 3 a duk fadin kasa daga jiya Juma'a, domin nuna alhinin ga wadanda harin ya rutsa da su.
Ya zuwa yanzu dai babu wata kungiyar da ta sanar da daukar alhakin kai harin. (Maryam)