Gwamnatin Najeriya ta yaba sakamakon rahoton da cibiyar nazarin tattalin arziki da zaman lafiya(IEP) ta wallafa game da matakan da ta ke dauka kan yaki ta ayyukan ta'addanci, kamar yadda hakan ke kunshe cikin rahoton cibiyar kan alkaluman yaki da ta'addanci na duniya na shekarar 2017.
Da yake karin haske cikin wata sanarwa da ya aike wa kamfanin dillancin labarai na Xinhua, ministan watsa labarai da al'adu na Najeriya Lai Mohammed, ya bayyana farin ciki da rahoton cibiyar, wanda ya nuna cewa, an samu raguwar kaso 80 cikin 100 na hasarar rayuka sakamakon hare-haren mayakan Boko Haram a shekarar 2016 da ta gabata, adadin da ya ragu da kaso 13 cikin 100 bisa makamancin lokaci na bara.
Ministan ya kara da cewa, shugaban cibiyar ta IEP Steve Killelea ya gamsu da nasarar da Najeriyar ta samu a yaki da ayyukan ta'addanci tun lokacin da shugaba Muhammadu Buhari ya hau kan karagar mulki a shekarar 2015.
Ya ce, Najeriya ta samu nasara a yakin da ta ke da ta'ddanci ne sakamakon irin jagorancin da shugaba Buhari ke gudanarwa, da kyayyawan yanayin da ya samarwa sojojin kasar na dawo martabarsu a wannan fanni, baya ga hadin gwiwar da Najeriyar da ta yi da kasashe makawabta, a kokarin ganin bayan kungiyar ta Boko Haram.
Lai Mohammed ya ce alkaluman yaki da ayyukan ta'addanci na duniya na wannan shekara da cibiyar ta wallafa, zai taimakawa gwamnati da sabbin matakai don ci gaba da zage damtse a kokarin da ta ke na kawar da kungiyar Boko Haram, tare da magance duk wasu ragowar matsaloli na rashin tsaro da kasar ke fuskanta.(Ibrahim)