A sanarwar bayan taron da aka fitar, an bayyana cewa, ta'addanci ya kawo barazana, da kalubale ga zaman lafiya da tsaro a dukkan sassan duniya, kuma kasashen musulmi su ne ke kan gaba wajen fuskantar wannan matsala.
Sanarwar ta kara da cewa, kasashe mahalarta taron sun tsai da kudurin yin hadin gwiwa da juna, da yaki da ta'addanci a fannonin warware hakikanin tunanin ta'addanci, da yada tunanin addini mafi dacewa, da yankewa kungiyoyin ta'addanci hanyoyin samun kudaden shiga, da kaddamar da hare-haren soja da dai sauransu, ta yadda za a kai ga murkushe ta'addanci baki daya.
An kuma tsai da kudurin cewa, za a gudanar da taron ministocin tsaron kasa da kasa na wannan kawance a kowace shekara, ko kuma a duk lokacin da bukatar hakan ta bijiro. (Zainab)