Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron, ya ba da jawabi jiya Labara a fadarsa cewar, tun daga farkon shekarar bana har zuwa yanzu, kasarsa ta riga ta dakile yunkurin farmaki 13. Ta'addanci kuwa shi ne barazana mafi tsanani ga tsaron kasarsa.
Ban da wannan kuma, shugaban Macron ya ce, a ko da yaushe kasarsa na cikin shirin ko-ta-kwana tun bayan watan Nuwamba na shekarar 2015. Amma daga ranar 1 ga wata mai zuwa, Faransa za ta kawar da dokar ta baci, sa'an nan za ta sa kaimi ga aikin yaki da ta'addanci ta hanyar aiwatar da sabuwar dokar yaki da ta'addanci.(Kande Gao)