Daraktan saashen yaki da ta'addanci na ma'aikatar, kuma kwamishinan 'yan sanda George Asiamah ne ya sanar da hakan, inda ya ce atisayen da za a fara ranar 25 ga wannan watan, zai kara karfafawa tare da yi wa jam'ai bitar kwarewarsu kan tunkarar hare-hare da shawo kansu.
Duk da cewa Ghana ba ta taba fuskantar hari ba, George Asiamah ya ce abubuwan dake faruwa a bayan-bayan nan a makwabtan kasashe na yankin da ma duniya baki daya, abun damuwa ne matuka, inda ya ce barazanar ta tilastawa Ghana daukar matakan tunkarar hare-haren ta'addanci.
Ya ce hukumomin tsaro sun fara shirin wayar da kan al'umma, da nufin ilmantar da su tare da shigar da hukumomin kai agaji cikin shirye-shiyen bitar inganta kwarewar aiki, ciki har da dabarun da suka zarce na tunkarar yaki da manyan makaman kare dangi, domin kasar ta zauna cikin shirin yaki da hare-haren ta'addanci. (Fa'iza Mustapha)