Ministan harkokin cikin gidan kasar Faransa Gerard Collomb, ya bayyana a jiya Lahadi cewa, hari da wuka da wani matashi ya kaddamar kan fararen hula, a tashar jiragen kasa ta Saint Charles dake birnin Marseille, na iya zama aikin ta'adanci, sai dai kuma ya bukaci a kai zuciya nesa har zuwa lokacin da za a tattara bayanai game da ainihin abun da ya faru.
Mr. Collomb ya yi Allah wadai da harin na yammacin jiya Lahadi, wanda ya bayyana a matsayin mummunar ta'asa, wadda ta kai ga rasa rayukan wasu mata su biyu. Tuni dai aka fara gudanar da bincike da nufin gano maharin, da ma wadanda harin ya rutsa da rayuwar su.
Wasu kafofin watsa labarai na yankin da lamarin ya faru, sun ruwaito cewa maharin dan kimanin shekaru 20, ya rika kabbara yayin da yake dabawa mutane wukar dake hannun sa. Kuma da ma can ya shahara wurin 'yan sanda, wajen aikata laifuka masu alaka da fashi da makami, da kuma safarar miyagun kwayoyi.
A nasa bangare shugaban Faransa Emmanuel Macron, ya nuna kaduwa game da aukuwar wannan aiki na keta. Cikin wani sako da ya dora a shafin sa na Twitter, ya yaba da yadda sojoji suka nuna sanin ya kamata da kwarewar aiki, yayin da suke shawo kan lamarin.
Wata sabuwa kuma, kamfanin dillancin labarai na kungiyar IS na Amaq ya ba da labarin cewa, kungiyar IS ta dauki alhaki kan aiwatar da wannan harin na ta'addanci.
Ana dai fuskantar yawan aukuwar hare haren ta'adanci a Faransa, a yayin da kasar ke daukar sabbin matakai na yaki da wannan matsala tun daga shekarar 2015, lokacin da mutane kusan 130 suka rasa rayukan su, kana wasu 350 suka jikkata, sakamakon wasu fashewa, da harbin kan mai uwa da wabi da kungiyar IS ta yi ikirarin kaddamarwa a kasar.(Saminu Alhassan)