in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gamayyar kasa da kasa sun yi allah wadai da harin da aka kai a Masar
2017-11-25 13:36:05 cri
Wasu kasashen duniya da kungiyoyin kasa da kasa sun yi Allah wadai da harin da aka kai a wani masallaci dake garin Al-Arish na lardin North Sinai dake arewacin kasar Masar a jiya Jumma'a.

Wata sanarwa da Babban Sakataren kawancen kasashen Larabawa ta LAS Ahmed Aboul Gheit ya fitar, ta ce, harin ya tayar musu da hankali matuka, kuma kawancen zai ba da goyon baya ga gwamnatin kasar Masar wajen yaki da ta'addanci.

Cikin Sanarwar da suka fitar bi da bi a jiya Juma'a, Kwamitin sulhu na MDD da Babban Magatakardan Majalisar Antonio Guterres, sun yi allah wadai da kakkausar harshe kan harin ta'addanci da aka kai a garin Al-Arish na lardin North Sinai.

Shi ma a nasa bangaren, shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya buga wa takwaransa na kasar Masar Abdel Fattah al Sisi waya, inda ya yi tir da harin, yana mai jaddada cewa kasarsa za ta hada gwiwa da Masar wajen yaki da ta'addanci.

Haka zalika fadar White House ta Amurka da majalisar gudanarwar kasar, su ma sun yi tir da harin, suna masu bayyana goyon bayansu ga Masar wajen yaki da ta'addanci.

Su ma kasashen Iraq da Bahrain da Yemen da Oman da Jordan da Turkiya da Burtaniya da Faransa da wasu kasashen duniya, ba a bar su a baya ba wajen yin Alla wadai da harin.

Rahoton kamfanin dillancin labarai na The Associated Press na kasar Amurka ya ruwaito cewa Isra'ila ma ta bayyana juyayi game da lamarin, inda ta ce, ya kamata gamayyar kasa da kasa su hada kai domin yaki da ta'addanci. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China