in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Masar da Sin za su karfafa kyakkyawar hulda a tsakaninsu
2017-11-07 09:53:16 cri
Wakilin musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping kuma ministan ilmin kasar Sin Chen Baosheng, ya bayyana cewa, kasar Sin tana fatar zurfafa kyakkyawar mu'amala da kasar Masar a dukkan fannoni da nufin daga martabar dangantakar dake tsakaninsu zuwa wani babban mataki.

Chen ya bayyana hakan ne a lokacin ganawa da shugaban kasar Masar Abdel-Fattah al-Sisi a lokacin taron dandalin matasa na kasa da kasa wanda ake gudanarwa har zuwa ranar 10 ga wannan watan.

Chen ya nanata cewa, a ko da yaushe kasar Sin tana yin garambawul game da yadda danganka ke gudana tsakanin kasashen Sin da Masar daga matsayin mu'amala ta dogon lokaci zuwa matsayin mu'amala ta kut da kut tsakanin bangarorin biyu. Ya kara da cewa kasar Sin a shirye take ta yi aiki tare da kasar Masar wajen aiwatar da yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin shugabannin kasashen biyu, da kuma zurfafa mu'amala tsakanin kasashen a dukkan fannoni don daga matsayin alakar dake tsakanin kasar Sin da Masar zuwa babban matsayi.

A nasa bangaren, shugaba al-Sisi ya bayyana cewa kasar Masar tana goyon bayan shawarar "ziri daya da hanya daya" wanda shugaba Xi ya gabatar, kana za ta yi aiki tare da kasar Sin wajen yin hadin gwiwa a fannin ci gaban masana'antu da sauran ayyukan cigaba. (Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China