in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Masar ta nada ministan gidaje a matsayin mai rikon mukamin firaministan kasar
2017-11-24 09:26:39 cri
Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi na kasar Masar ya nada ministan gidaje Mostafa Madbouli a matsayin mai rikon mukamin firaministan kasar, Sherif Isma'il wanda ya je jinya a kasar Jamus.

Da yake Karin haske kan lamarin, mai Magana da yawun majalisar zartarwar kasar Ashraf Sultan ya karyata rahotanni da ke cewa, Isma'il na fama da wani tsiro ko wata cuta mai alaka da hakan.

A nasa bangare Madbouli ya sanar a jiya cewa, shugaba Abdel Fattah al-Sisi shi ne ya nada shi rikon mukamin firaministan kafin Isma'il ya dawo daga jinyar da ya je yi a kasar Jamus.

Shi dai Isma'il ya rike mukamin ministan mai a sabuwar gwamnatin da aka kafa, bayan hambarar da gwamnatin Mohammed Morsi a watan Yulin shekarar 2013, kafin daga bisani shugaba Sisi ya nada shi a matsayin firaministan kasar ta Masar a tsakiyar watan Satumbar shekarar 2015.

A watan Yunin sheakarar 2015, an nada ministan sufuri na kasar a matsayin mai rikon mukamin ministan mai don maye gurbin Isma'il lokacin da ya yi tafiya, amma kuma gwamnati a wancan lokaci ba ta yi wani Karin haske ko dalilinta na daukar wannan mataki ba. A farkon watan Agustan wannan shekara ce, Isma'il ya yi tafiyar kwanaki biyu zuwa kasar Jamus domin a duba lafiyarsa, lamarin da ya jefa ayar tambaya game da koshin lafiyarsa, amma a kullum gwamnati na cewa, ba abu ne na daga hankali ba.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China