An gudanar da zaben ne a lokacin babban taron UNESCO karo na 39 a birnin Paris.
Kasar Masar, ta taba zama mamba a UNESCO daga shekarar 2013 zuwa 2017, Masar ta samu kuri'u 141 daga cikin kuri'u 184 da aka kada a tsakanin kasashen Masar din da Iraq, da Jordan, da kuma kasar Morocco.
Kasashen yankin larabawa 4 ne suka fafata a kujeru 3. Jordan ce ta zama ta farko da kuri'u 153, Masar ta zama ta biyu da kuri'u 141, Morocco ta uku da kuri'u 125 sai kuma Iraq da kuri'u 109.
A wata sanarwa da ma'aikatar harkokin wajen kasar Masar ta fitar ta bayyana cewa, Masar ta sake samun nasara a matsayin mamba a hukumar ta kasa da kasa ne sakamakon irin rawar da take takawa a harkokin diplomasiyya da kuma raya al'adu a mataki na kasa da kasa. (Ahmad Fagam)