Taron yini biyu na kwamitin kwararrun kasashen Masar da Habasha da Sudan kan madatsar ruwan Habasha ta GERD da aka fara a ranar Asabar, ya gaza amincewa da wani rahoton bayani da wani kamfanin tuntuba ya yi game da tasirin Madatsar kan kasashen Sudan da Masar.
Ministan albarkatun ruwa da noman rani na Masar Mohammed Abdel-Aati, ya ce kasarsa ta damu da rashin nasarar taron wanda zai kawo tsaiko ga nazarin na kwararru, duk da kokarin kasarsa cikin watannin da suka gabata na tabbatar da an kammala nazarin cikin lokaci.
Ministocin Habasha da Sudan sun ki amincewa da rahoton kamfanin tuntubar, duk da amincewa da shi da Masar ta yi tun da farko, inda suka nemi wasu gyare-gyare da za su shafi rahoton tare da mayar da shi maras ma'ana.
Masar ta damu ne da kasonta na kubik mita biliyan 55.5 na ruwan Kogin Nile yayin da ake tsaka da ginin madatar ruwan GERD. (Fa'iza Mustapha)