in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
MDD ta yi tir da harin ta'addanci a Masar
2017-10-22 12:23:50 cri

Kwamitin tsaron MDD ya yi Allah wadai da babbar murya game da harin ta'addanci da aka kaddamar ranar Jumma'a a saharar El Wahat dake kasar Masar, lamarin da ya hallaka jami'an 'yan sanda masu yawa ya kuma jikkata wasu da dama.

Cikin wata sanarwa da shugaban kwamitin tsaron MDD Francois Delattre, ya rabawa manema labarai, mambobin sun bayyana matukar juyayinsu tare da mika sakon ta'aziyya ga gwamnatin Masar da iyalan wadanda harin ya rutsa da su, kana sun yi fatan samun sauki cikin hanzari ga wadanda suka samu raunuka a harin.

Kwamitin MDD ya jaddada aniyarsa na gudanar da bincike domin bankado wadanda ke da hannu wajen aikata harin, da wadanda ke daukar nauyin shirya harin ta'addancin, domin gurfanar da su a gaban shari'a, kwamitin ya bukaci dukkanin jahohi da su hada kai da gwamnatin Masar da kuma dukkan bangarorin da abin ya shafa domin cimma wannan buri.

Bugu da kari, kwamitin tsaron ya bayyana ta'addanci a matsayin wani mummunan laifi wanda ya kasance babbar barazana ga tsaro da zaman lafiyar kasa da kasa, inda ya nemi dukkan jahohi da su yi iyakar bakin kokarinsu domin magance barazanar tsaro da zaman lafiya wanda ta'addancin ke haddasawa.

A kalla 'yan sanda 54 ciki har da manyan jami'ai 20 da kurata 34 ne suka mutu a harin, a lokacin da mayaka masu dauke da makamai suka yi musu kofar rago a kudu maso yammacin birnin Alkahira. Jami'ai a kasar sun tabbatar da cewa, wannan shi ne hari mafi muni da aka taba kaddamarwa kan jami'an tsaron kasar Masar cikin 'yan shekarun nan.(Ahmad Fagam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China