Geng Shuang ya ce da yake taya Emmerson Mnangagwa murnar kama aiki, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce kasar Sin da Zimbabwe abokan arziki juna ne cikin shekaru da dama da suka gabata, inda ya ce kasashen biyu za su ci gaba da raya dangantakar abota dake tsakaninsu.
Ya kara a cewa, Kasar Sin tana mai da hankali sosai kan zumuncin dake tsakaninta da Zimbabwe, kuma tana son karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu ta fuskoki daban daban, domin kara tallafawa al'ummominsu. (Maryam)