in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaba Mugabe na Zimbabwe zai jagoranci taron majalisar zartarwa a yau Talata
2017-11-21 10:50:35 cri
Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe, zai jagoranci zaman majalisar zartarwar kasar da aka saba yi a yau Talata, ranar da jam'iyyarsa za ta fara yunkurin tsige shi a majalisar dokokin kasar.

Kafar yada labarai ta kasar ZBC ta ruwaito a jiya Litinin cewa, sakataren gwamnatin kasar na gayyatar dukkan mambobin majlisar don halartar taron.

A kan gudanar da taron ne a gidan Gwmanatin kasar da ake wa lakabi da Munhumutapa.

A jiya Litinin ne 'ya'yan jam'iyyar da suka fi rinjaye a majalisar dokokin kasar suka amince da matakin jam'iyyar na tsige Shugaba Mugabe, bayan wa'adin da aka dibar masa don ya yi murabus ya cika ba tare da ya yi ba. Kakakin jam'iyyar Khayo Moyo, ya ce 'ya'yan Jam'iyyar dake majalisar 230 daga cikin 260 sun amince da tsige shugaban kasar.

Yayin zaman majalisar na yau Talata ne jam'iyyar za ta gabatar da kudurin neman tsige Robert Mugabe. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China