in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Zimbabwe mai jiran gado ya yi kira ga al'ummar kasar su kauracewa ramuwar gayya
2017-11-24 09:13:56 cri
Shugaban kasar Zimbabwe mai jiran gado Emmerson Mnangagwa, ya bukaci al'ummar kasar su ci gaba da zaman lafiya tare da kauracewa daukar fansa a tsakaninsu.

Da yake jawabi a jiya Talata ta kafar yada labaran kasar ZBC, Emmerson Mnangagwa, ya ce ramuwar gayya ba ta daga cikin dabi'un al'ummar kasar.

Ya ce yayin da al'amura ke ci gaba da wakana, yana bukatar al'umma su kasance masu hakuri su kuma kauracewa duk wani nau'i na daukar fansa. Inda ya kuma yi kira da su guji sabawa doka wajen warware rikice-rikice.

A yau Juma'a ne za a rantsar da sabon shugaban kasar, inda zai kammala sauran wa'adin mulkin tsohon shugaba Robert Mugabe, wanda ya yi murabus a ranar Talata da ta gabata bayan ya fuskanci matsin lamba daga sojoji da al'ummar kasar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China