in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe mai jiran gado ya yabawa sojoji da 'yan kasar
2017-11-23 10:14:10 cri

A jiya ne shugaban kasar Zimbabwe mai jiran gado Emmerson Mnangagwa ya yi bayyanarsa ta farko a bainar jama'a, bayan dawowarsa kasar daga gudun hijira. A jawabin da ya gabatar wa magoya bayansa, Mnangagwa ya ce, ya yi matukar farin ciki da irin kauna da goyon bayan da sojoji da 'yan kasar suka nuna masa, tun bayan da tsohon shugaban kasar Robert Mugabe ya tsige shi daga mukaminsa makonni biyu da suka gabata.

Mnangagwa wanda ya yi alkawarin bautawa jama'a, ya kuma bukaci daukacin 'yan kasar Zimbabwe su hada kai don gina tattalin arzikin kasar, a wani mataki na samun zaman lafiya da kara kirkiro guraben ayyukan yi ga 'yan kasa.

Ya ce, Zimbabwe ta bude wani sabon babi na demokuradiya, bayan da sojojin kasar suka taimaka wajen kawar da tsohon shugaban kasar da ya dade yana mulkin kasar, kuma yanzu haka ya fara samun sakonnin goyon baya daga kasashen duniya da dama.

A gobe Jumma'a ne ake saran za a rantsar da Mnangagwa a matsayin shugaban kasar ta Zimbabwe, a don haka ya bukaci samun goyon bayan kasashen duniya, domin sake farfado da tattalin arzikin kasar da ya durkushe.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China