Shugaba Mnangagwa ya maye gurbin Robert Mugabe, wanda ya yi murabus daga jagorancin kasar sakamakon matsin lamba da ya sha, bayan shafe shekaru 37 yana jagorancin Zimbabwe.
Tsohon shugaban kasar Robert Mugabe, ya jagoranci Zimbabwe tun daga shekara ta 1980, bayan da kasar ta samu 'yancin kai daga Turawan mulkin mallaka.
Yayin rantsuwar kama aikin wadda babban jojin kasar Luke Malaba ya jagoranta, Mnangagwa ya alkawarta biyayya ga kundin tsarin mulkin kasarsa, da kuma kare hakkokin al'ummar Zimbabwe. (Saminu Hassan)