in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin: Mugabe, abokin arziki ne na kasar Sin
2017-11-22 20:19:08 cri

Da yammacin yau Laraba ne kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Lu Kang, ya bayyana a nan Beijing cewa, kasar Sin ta girmama kudurin da mista Robert Mugabe ya tsai da na yin murabus. Kuma tsohon shugaban na Zimbabwe abokin arziki ne na kasar Sin.

Da yammacin ranar Talata ne dai bisa agogon kasar Zimbabwe, shugaba Robert Mugabe ya sanar da yin murabus. Bayan haka, kasashen Birtaniya da Amurka sun yi kira ga Zimbabwe, da ta gudanar da babban zabe cikin adalci da 'yanci.

Dangane da lamarin, a yayin taron manema labaru da aka saba shiryawa a nan Beijing, Lu Kang ya ce, har kullum kasar Sin na tsayawa kan akidar rashin tsoma baki cikin harkokin cikin gida na sauran kasashen duniya. Tana kuma girmama zabin da jama'ar Zimbabwe za su yiwa kan su. Kaza lika asar Sin ta yi imani da cewa, jama'ar Zimbabwe za su iya daidaita batunsu yadda ya kamata, kana kuma kasar Sin na fatan ba za a tsoma baki cikin harkokin cikin gidan kasar ta Zimbabwe ba. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China