Jiya Laraba ne Xie Xiaoyan, wakilin musamman na kasar Sin mai kula da batun kasar Syria,ya gana da Staffan de Mistura, wakilin musamman na babban sakataren MDD mai kula da batun Syria, a birnin Geneva, inda suka yi musayar ra'ayoyi kan yadda za a daidaita batun Syria a siyasance da kuma tattaunawar zaman lafiya da zai gudana a Geneva nan ba da dadewa ba.
Yayin ganawar, Xie Xiaoyan ya yi karin bayani kan matsayin kasar Sin game da batun Syria, inda ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi maraba da shirin MDD na tattauna batun zaman lafiya a Geneva, tsakanin sassa daban daban na Syria.
Mista Xie ya kuma jaddada cewa, kasar Sin ta na marawa MDD baya a kokarinta na jagorantar batun shiga tsakani game da rikicin Syria.
Har ila yau, ya ce kasar Sin ta tsaya tsayin daka wajen ganin al'ummar Syria sun warware batun kasarsu da kansu.
A nasa bangaren, Mista Mistura ya yi nuni da cewa, MDD ta yaba wa kasar Sin sosai kan adalci da take nunawa, ta hanyar tsayawa bisa sanin ya kamata kan batun na Syria, da kuma kokarin da take yi wajen daidaita batun ba tare da jan jiki ba. (Tasallah Yuan)