in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da takwaransa na Zimbabwe
2017-01-09 20:35:09 cri

A yau Litinin ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da takwaransa na Zimbabwe Robert Mugabe a birnin Beijing.

A yayin ganawarsu, shugaba Xi ya jaddada cewa, bisa kokarin bangarorin biyu, shi da shugaba Mugabe sun cimma matsaya kan raya dangantaka tsakanin kasashen biyu da tabbatar da sakamakon da aka samu a taron kolin Johannesburg na dandalin tattaunawar hadin gwiwa tsakanin Sin da kasashen Afirka. Bugu da kari, sassan biyu suna hadin gwiwa yadda ya kamata a fannonin samar da muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a da aikin gona da sauransu. Sin na fatan sa kaimi ga kamfanonin kasar su je kasar Zimbabwe domin zuba jari da zurfafa hadin gwiwa tsakaninsu. Haka kuma Sin na fatan fatan raya dangantakar hadin gwiwa da samun moriyar juna tsakaninta da Zimbabwe.

A nasa bangare, shugaba Mugabe ya bayyana cewa, ya yi farin cikin sake zuwan kasar Sin. Ziyarar da shugaba Xi ya kai Zimbabwe a shekarar 2015, da halartar taron kolin Johannesburg sun samu babbar nasara. Sin ta dade tana taimakawa kasashen Afirka, ciki har da kasar Zimbabwe ta fannin raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma. Yanzu kasashen Afirka suna kokarin daukar matakai domin tabbatar da shirin hadin gwiwa guda 10 da shugaba Xi ya gabatar a taron kolin Johannesburg. Yana fatan kasar Zimbabwe za ta ci gaba da zurfafa hadin gwiwa tsakaninta da Sin a fannonin muhimman kayayyakin more rayuwar jama'a da aikin gona da dai sauransu.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China