Ministar kwadago da walwalar jama'a ta Zimbabwe Prisca Mupfumira, ta ce za kuma a raba gudunmuwar da kasar ta samu bayan neman taimakon kasashen duniya da ta yi a shekarar 2016, ga iyalan da ambaliyar ruwa ta shafa a watan Fabrairun bana.
Da take jawabi a ofishin jakadancin Sin dake Zimbabwe, Mupfumira ta ce ana sa ran shinkafar za ta isa kasar cikin watan Yuni mai zuwa.
Bayan neman gudunmuwar a shekarar 2016, Kasar Sin ta ba Zimbabwe gudunmuwar ton 19,000 na shinkafa, inda aka raba ga mabukata a fadin kasar.
Wannan na zuwa ne bayan Sin ta mika gudunmuwar dalar Amurka miliyan 1 ga kasar a ranar 31 ga watan Maris, domin taimakawa mutanen da ambaliya ta shafa a kudancin kasar.
Mupfumira ta kara da cewa gwamnatin Zimbabwe ta raba ton 481,073 na masara ga mabukata a cikin watan Oktoban bara.
Ruwa da aka yi kamar da bakin kwarya da guguwa a kasar cikin watan Fabrairu, ya yi sanadin rayukan mutane 271, yayin da ya raunata wasu 128 tare da raba kusan mutane 2,000 da matsugunansu. (Fa'iza Mustapha)