in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta musunta zargin 'biyan bashi da giwaye'
2016-12-29 19:00:32 cri
Wasu kafofoin watsa labaru na kasashen waje sun ba da labarin cewa, kasar Zimbabwe ta sayar da wasu namun daji da suka hada da giwaye da zakuna ga wani gidan dabbobi na kasar Sin, a matsayin biyan bashin da kasar Sin take bin kasar bayan da ta sayi wasu rigunan sojoji daga kasar Sin don tallafawa kasar Kongo Kinshasa. Dangane da batun, Madam Hua Chunying, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, ta sanar a nan birnin Beijing fadar mulkin kasar Sin, a yau Alhamis, cewa babu gaskiya a cikin wannan labarin ko kadan.

A cewar Madam Hua, hakika wasu gidajen dabbobi dake biranen Shanghai, Beijing, da Hangzhou na kasar Sin sun sayi wasu giwaye 35 daga hannun mahukuntan kasar Zimbabwe, a kwanakin baya. Kuma an biya mahukuntan kasar Zimbabwe kudin, wadanda za a yi amfani da su wajen samar da kariya ga namun dajin kasar.

Kakakin kasar Sin ta nanata cewa, wannan batun ne na kasuwanci, kuma ya dace da yarjeniyoyin kasa da kasa da dokokin kasashen Sin da Zimbabwe. Don haka labarin da wasu kafofin watsa labaru suka watsa ba shi da tushe, kuma an tsara shi ne bisa buri maras kyau.

Jami'ar ta ce wasu gidajen dabbobi a wasu wurare daban daban na duniya, sun saba irin wannan aiki na shigo da namun daji daga ketare. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China