in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yawan wadanda suka rasu sakamakon harin kunar bakin wake a Adamawa ya kai mutum 40
2017-11-21 19:36:23 cri

Ya zuwa yanzu yawan wadanda suka rasu, sakamakon harin kunar bakin wake da ya auku a wani masallaci dake unguwar Kunu Araha dake wajen garin Mubin jihar Adamawa, a arewa maso gabashin Najeriya ya kai mutum 40.

A cewar ma'aikatan ba da agajin gaggawa na yankin, tuni aka debe wadanda harin na Asubahin yau Talata ya rutsa da su. Da fari dai mutum 30 ne aka tabbatar da rasuwarsu, kafin adadin ya karu yayin da ake aikin ceton rayukan wadanda suka ji raunuka.

Da yake karin haske game da aukuwar lamarin, kakakin rundunar 'yan sandan jihar ta Adamawa Othman Abubakar, ya ce wani matashi ne ya kutsa kai cikin masallacin sanye da damarar ababen fashewa, ya kuma tada ababen fashewar a tsakiyar masallacin.

Unguwar Kunu Araha dai na wajen garin Mubi.

Kawo yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kaddamar da wannan hari, sai dai kuma jami'an tsaro, da mazauna yankin na zargin mayakan Boko Haram da aikata wannan ta'asa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China