in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Gwamnan jihar Bayelsa a Najeriya ya gargadi dora dan takarar da jama'a ba sa so
2017-11-10 09:13:40 cri

Gwamnan jihar Bayelsa mai arzikin man fetur a tarayyar Najeriya Seriake Dickson ya gargadi jam'iyyar PDP mai adawa da ta guji dora dan takara da karfin tsiya, yayin da jam'iyyar ke shirye-shiryen gudanar da babban taron wakilanta na kasa a ranar 9 ga watan Disamba, inda ake sa ran zaben shugabannin jam'iyyar na kasa.

Dickson wanda shi ne tsohon shugaban kamitin sassantawa na jam'iyyar PDP, ya kuma bukaci shugabannin jam'iyyar ta PDP da wakilai, da su yi kokarin hada kan 'yayan jam'iyyar ta yadda za ta kai ga nasara.

Gwamnan wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da aka rabawa manema labarai a birnin Legas, cibiyar kasuwancin kasar, ya ce, kamata ya yi a bar 'yan takara su nuna farin jininsu a lokacin babban taron jam'iyyar. Idan har shugabanni da wakilan jam'iyyar suka kasa cimma matsaya kan duk wani mukami. Yana mai cewa, yi wa 'yan takara adalci shi ne kadai zai kara hada kan jam'iyyar.

A don haka ya ce, bai kamata babban taron ya sake haifar da wata sabuwar baraka ga jam'iyyar ta PDP ba. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China