in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Nijeriya ya aike da sakon ta'aziyya ga Iran
2017-11-18 13:25:05 cri
Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari, ya jajantawa shugaban Iran Hassan Rouhani da al'ummar kasar, game da dimbin asarar rayuka da girgizar kasar da ta aukawa kasar ta haifar.

Wata sanarwa da Kakakinsa Garba Shehu ya fitar, ta bayyana girgizar kasa da aka yi a yammacin lardin Kermanshah na Iran a matsayin mai ciwo matuka.

Sanarwar ta kuma bayyana iftila'in da asarar da ya haifar a matsayin abun bakin ciki mai tada hankali.

Shugaba Muhammadu Buhari ya kuma mika irin wannan jaje ga Gwamnati da al'ummar Iraqi bisa asarar dukiya da rayuka da suka yi sanadiyyar girgizar kasar da ta auku akan iyakar kasar da Iran. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China