in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar 'yan sandan Nijeriya ta tura jiragen ruwa masu bindiga don magance fashin teku a yankin dake da arzikin man fetur
2017-11-20 11:01:38 cri
Rundunar 'yan sandan jihar Bayelsa mai arzikin mai a Nijeriya, ta tura jiragen ruwa 16 masu dauke da bindigogi da 'yan sanda 6,000 domin magance fashin teku da sauran laifukan da ake aikatawa cikin ruwa, da nufin tabbatar da tsaron hanyoyoin ruwan.

Kwamishinan 'yan sandan jihar Asuquo Amba, ya ce an tura jami'an 6,000 ne bayan an horar da su kan aiki cikin ruwa, yayin da har yanzu ake horas da wasu.

Kwamishinan ya ce rahotannin sirri da rundunar ta tattara, sun bayyana cewa an samu kyautatauwar al'amura a jihar Delta da kogunan dake jihar sanadiyyar hadin gwiwar da aka yi tsakanin hukumomin tsaro na jihar.

Ya kuma tabbatar da cewa, har yanzu akwai kalubalen fashin teku da ake fuskanta a jihar, ya na mai alkawarin nan bada dadaewa ba, rundunarsu za ta yi maganin 'yan fashin dake addabar hanyoyin ruwan jihar.

Asuquo Amba, ya ce Gwamnatin jihar ce ta gyara 14 daga cikin jiragen ruwa 16 da aka tura, yayin da rundunar ta samar da guda 2.

Bayelsa na daga cikin wurare masu arzikin danyen man fetur da iskar gas a kasar dake yammacin Afrika, wadda ita ce ta fi kowacce samar da man fetur da kuma yawan al'umma a nahiyar. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China