in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Nijeriya za ta yi bincike game da mutuwar 'yan kasar 26 a tekun Bahar Rum
2017-11-10 09:04:35 cri

Majalisar dattawan Nijeriya, ta ce za a gudanar da bincike kan mutuwar 'yan kasar 26 a tekun Bahar Rum a farkon makon nan.

A wani kuduri da aka gabatar yayin zamanta jiya a Abuja, babban birnin kasar, Majalisar ta ce, kwamitin da ya kunshi hukumomin da suka hada da ta harkokin waje da ta kula da shige da fice da hukumar hana safarar bil Adama, zai fara aiki nan take don binciken al'amarin.

A cewar majalisar, masu bincike na kasar Italiya sun tsare mutane biyu da ake zargi da suka hada da dan kasar Masar da dan kasar Libya.

Majalisar ta kara da cewa, ya zama wajibi a yi bincike kan mutuwar 'yan kasar mata, tana mai cewa a cikin watan Mayun da ya gabata, kimanin 'yan Nijeriya 10,000 ne suka mutu a kan hanyar hamadar Sahara zuwa Libya zuwa tekun Bahar Rum.

A ranar Talata da ta gabata ne Gwamnatin kasar ta tabbatar da mutuwar 'yan kasar 26, galibinsu matasa, inda ta ce sun nutse cikin tekun Bahar Rum a ranar Lahadin da ta gabata. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China