in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzkin Nijeriya ya daga da kaso 1.4 cikin rubu'i na 3 na bana
2017-11-21 10:46:36 cri
Hukumar tattara alkaluman kididdiga ta Nijeriya, ta ce alkaluman tattalin arzikin kasar wato GDP sun daga da kaso 1.4 cikin rubu'i na 3 na bana, idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara.

Rahoton da hukumar ta fitar a jiya ya nuna cewa, tattalin arzikin kasar ya samu tagomashi sau biyu a jere, tun bayan fitar kasar daga matsin tattalin arziki a rubu'i na biyu na bana, inda bangarorin man fetur da noma da na masana'antu suka taka muhimmiyar rawa wajen samar da wannan ci gaba.

Habakar da ta kai kaso 3.74 ta dara kaso 2.34 da aka samu a rubu'i na 3 na bara. Haka zalika, ya dara kan na rubu'in na 2 da kaso 0.68, wanda ya kai 0.72 daga kaso 0.55.

Cikin watan Satumban da ya gabata ne Nijeriya ta fita daga matsin tattalin arziki mafi muni da ta taba shiga cikin gomman shekaru da suka gabata.

Da take mai da martani game da alkaluman, Gwamnatin kasar ta bayyana shi a matsayin alamu dake nuna nasarorin da tattalin arzikin kasar ke samu.

Sanarwar da wani kakakin fadar shugaban kasar ya fitar, ta ce Gwamnati na aiki tare da jajircewa wajen aiwatar da manufofi don tabbatar da an samu ci gaba na bai daya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China