Wu Haitao ya ce, kasar Sin na da ra'ayin cewa, ya kamata a tsai da kudurin da zai ba da taimako ga kasashen da abin ya shafa, ta yadda za su warware matsalolinsu cikin hadin gwiwa. A sa'i daya kuma, za a iya yin gyare-gyare kan kudurin bisa yanayin da ake ciki.
Mambobin kwamitin suna da bambancin ra'ayoyi kan kuduri mai lamba 2385, wanda kwamitin ya zartas, lamarin da ya nuna cewa, ya dace a kyautata kudurin, wanda hakan ne ya sanya kasar Sin ta janye jiki daga gare shi. (Maryam)