in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu na MDD ya jadadda bukatar kare yara a inda ake yake-yake
2017-11-01 10:45:03 cri
Kwamitin sulhu na MDD ya jadadda muhimmancin kare yara a wuraren da ake yake-yake tare da neman kare hakkokinsu a irin wannan yanayi.

Sanarwar da kwamitin ya fitar a jiya Talata, ta ce kamata ya yi kare yara a inda ake yaki ya zama muhimmim mataki na warware rikici da tabbatar da zaman lafiya.

Kwamitin ya kuma bukaci bangarorin dake rikici da juna, su dauki dukkan matakan kare fararen hula da kadororin fararen hulan dake karkashin ikonsu, kamar yadda dokokin kare hakkin dan Adam na duniya suka tanada.

Har ila yau, sanarwar ta jadadda yin tir da kakkausar murya, kan amfani da yara da bangaroi masu rikici ke yi tare da horar da su, da kashe-kashe da fyade da duk wani nau'i na cin zarafi, da sace mutane ko garkuwa da su da farwa makarantu ko asibitoci, ta na mai bukatar dukkan masu rikici su kauracewa wadannan dabi'u. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China