in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin Sin ya bayyana ra'ayin Sin kan batun 'yan sandan kiyaye zaman lafiya na MDD
2017-11-07 16:03:12 cri
Mukadashin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Wu Haitao, ya bayyanawa kwamitin sulhu na MDD ra'ayin kasar Sin dangane da 'yan sandan kiyaye zaman lafiya na majalisar.

Wu Haitao wanda ya gabatar da jawabi ga kwamitin a jiya Litinin, ya ce, a halin yanzu, 'yan sandan kiyaye zaman lafiya na MDD suna fuskantar kalubale iri daban daban, inda ya ce, ya kamata gamayyar kasa da kasa su tattauna kan yadda za a tunkari matsalolin, yayin da ake kokarin kyautata tsarin gudanarwar ayyukan 'yan sandan, domin samar da ci gaba a wannan fanni. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China